Tawagar ‘yan wasan Super Eagles sun sauka a birnin Kumasi, wurin da za su kara da Black Stars ta Ghana.
Super Eagles sun sauka a ranar Alhamis dinnan wanda za su nemi gurbin shiga gasar cin kofin duniya ta 2022 da aka shirya gudanarwa a yammacin Juma’a.
Tawagar da ta kunshi ‘yan wasa 25 da kwararrun ma’aikatan jirgin da sauran jami’an hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF a safiyar Alhamis, ta tashi daga filin jirgin saman Nnamdi Azikwe International Abuja a cikin jirgin Air Peace.
Za a fara wasan ne da misalin karfe 8:30 na dare agogon Najeriya ranar Juma’a a cikin filin wasa na Baba Yara da ke Kumasi.