Yayin da Senegal da Netherlands suka samu ketarawa zagayen kwaf daya a rukunin A, da kuma Ingila da Amurka a rukunin B na gasar cin kofin duniya a Qatar, idan anjima ne za a san kasashen da za su fito a rukunin C da D.
Senegal ta samu tsallakewa ne bayan ta doke Ecuador 2-1, inda ta zo ta biyu da maki shida.
Sai kuma Netherlands ta daya da maki bakwai bayan doke mai masaukin baki wato Qatar.
A yanzu za a hadu Ingila da Senegal, Netherlands kuma da Amurka a zagayen kwaf daya.
Idan anjima kuma za a san kasashen da za su tsallake, tsakanin Argentina da Poland da Saudiyya da kuma Poland a rukunin C.
Kazalika za a san kasar da za ta raka Faransa, tsakanin Tunisia da Denmark da Australia.