Sadio Mane ba zai buga wasannin farko na gasar cin kofin duniya da Senegal za ta buga saboda rauni, in ji wani jami’in hukumar kwallon kafar Senegal a ranar Talata.
Matsayin dan wasan gaban Bayern Munich a Qatar 2022 da alama ya na cikin hadarim bayan ya samu raunin a kafarsa a watan, amma an saka shi cikin ‘yan wasa 26 na mai horaswar Senegal Aliou Cisse.
Sai dai Mane ba zai buga karawar da Senegal za ta yi da Netherlands a ranar litinin mai zuwa ba, kuma mamba a hukumar kwallon kafar Senegal Abdoulaye Sow, ya bayyana cewa ba zai kasance a rukunin A kadai ba.
A ranar Alhamis mai zuwa ne Senegal za ta kara da Qatar mai masaukin baki kafin ta kara da Ecuador a wasan karshe na rukuni a ranar 29 ga watan Nuwamba.
Sow ya ce: “Senegal za ta iya jurewa ba tare da dan wasanta na farko ba.
“Dole ne mu dogara da buga wasannin farko ba tare da Sadio ba kuma mu yi nasara ba tare da Sadio ba saboda muna da ‘yan wasa 25 ban da Sadio.
“Ba wanda zai so, amma abin da ya faru da mu ke nan.”
Mane ya taka rawar gani a lokacin da Senegal ta lashe gasar cin kofin Afrika a bana kuma ya fara taka leda a Bayern bayan ya koma Liverpool.
Raunin mai shekaru 30 zai hana shi karawa da tsohon abokin wasansa na Liverpool, Virgil van Dijk mako mai zuwa.