Za a gudanar da gasar cin kofin duniya na 2022 a kasar Qatar daga ranar 21 ga watan Nuwamba zuwa 18 ga Disamba.
Za a kwashe kwanaki 27 a na gudanar da gasar ne a filayen wasanni takwas. Zai kasance gasar kwallon kafa ta farko da za a yi a Gabas ta Tsakiya.
Kungiyoyi 15 ne suka fito ciki har da masu masaukin baki da samu tikitin shiga gasar cin kofin duniya mai kungiyoyi 32 kawo yanzu:
- Qatar
- Argentina
- Belgium
- Brazil
- Croatia
- Denmark
- England
- France
- Germany
- Iran
- The Netherlands
- Serbia
- South Korea
- Spain
- Switzerland
- Za a gudanar da jadawalin gasar cin kofin duniya a Doha babban birnin Qatar a ranar 1 ga Afrilu.Kungiyoyi biyar ne za su fito daga nahiyar Afrika wadanda suka yi nasara a wasannin share fage na biyu a watan Maris da za su wakilci Afirka a Qatar 2022.
Masar da Senegal
Kamaru v Algeria
Najeriya da Ghana
DR Congo da Maroko
Mali v TunisiaDaga yankin Asiya kuwa kungiyoyi biyar ko shida ne za su fito, dangane da sauran wasannin share fage, za su wakilci Asiya.
A cewar hukumar ta FIFA, kungiyoyi biyu na farko a kowace rukuni za su haye da kungiyoyin da ke matsayi na uku a kowane bangare, inda za su hadu a wasa daya, domin samun damar shiga wasannin neman shiga gasar cin kofin duniya.
A bangaren Turai a baya 10 ne suke cancanta, akwai wasu guraben karo uku da za su fafata a kungiyoyin Turai.
Wadanda suka cancanci buga wasan akwai: Austria, Czech Republic, Italiya, Arewacin Macedonia, Poland, Portugal, Rasha, Scotland, Sweden, Turkiyya, Ukraine da Wales.