Shugaban kungiyar Black Stars ta Ghana, Otto Addo, a ranar Litinin ya bayyana jerin sunayen ‘yan wasa 26 na karshe da zai wakilci kasar a gasar cin kofin duniya ta FIFA 2022 a Qatar.
Addo ya hada da Thomas Partey na Arsenal, da Iñaki Williams na Athletic Bilbao, da sauran su a cikin tawagar.
Ghana tana rukunin H a gasar cin kofin duniya ta Qatar 2022 tare da Portugal, Uruguay da Koriya ta Kudu.
Tawagar Ghana a gasar cin kofin duniya:
Masu tsaron gida: Lawrence Ati-Zigi, Abdul Manaf Nurudeen, Ibrahim Danlad.
Masu tsaron baya: Denis Odoi, Alidu Seidu, Tariq Lamptey, Daniel Amartey, Joseph Aidoo, Alexander Djiku, Mohammed Salisu, Abdul Rahman Baba, Gideon Mensah
Dan wasan tsakiya: Andre Ayew, Thomas Partey, Mohammed Kudus, Elisha Owusu, Salis Abdul Samed, Daniel Kofi Kyereh, Daniel Afriyie Barnieh, Kamal Sowah, Osman Bukari, Abdul Fatawu Issahaku, Kamaldeen Sulemana
‘Yan wasan gaba: Iñaki Williams, Antoine Semenyo, Jordan Ayew