fidelitybank

Putin ya kori babban Janar saboda gazawa a kan Ukraine

Date:

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya kori wani babban Janar mai kula da kayayyakin bukatun sojin kasar da ke yaki a Ukraine.

Ma’aikatar tsaron kasar ta ce an kori Janar Dmitry Bulgakov – wanda shi ne mataimakin ministan tsaron kasar – ranar Asabar.

Janar Bulgakov shi ne mai kula da kayayyakin bukatun sojin kasar tun shekarar 2008, kuma shi ne mai kula da sayan kayyakin bukatun sojin kasar da aka kai Siriya a shekarar 2015.

Masu sanya ido na cewa a ‘yan watannin nan kasar ta ajiye shi a gefe, inda wasu da dama ke zarginsa da rashin ingantaccen tsarin kula da kayayyakin aikin soji, abin da kuma suka ce, shi ne ke kawo koma-baya ga ayyukan sojin kasar a Ukraine saboda rashin wadatattun makamai.

A ‘yan watannin nan dai kasar kan sayo makaman atilari, da jirage marasa matuka, daga Koriya ta arewa da Iran sakamakon takunkumai da take fuskanta a sauran kasashe.

Korar Janar Bulgakov na zuwa ne bayan da wani faifan bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta a kasar ya nuna yadda ake bai wa sabbin sojojin kasar bindigogi kirar AK-47.

Masu goyon bayan yakin da kasar ke a Ukraine sun nuna jin dadinsu kan karor babban jami’ain sojin, tare da nuna jin dadinsu kan maye gurbinsa da janar Mizintsev – wanda Birtaniya ta sanya wa takunkumi kan jagorantar kwace birnin Mariupol.

vanguard newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp