Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, ya taya sojojin Rasha murnar samun nasara a yankin Luhansk na kasar Ukraine.
A wani taro da kafar yada labaran Rasha ta yada a ranar Litinin, ministan tsaron kasar Sergei Shoigu ya shaidawa Putin ci gaban da Rasha ta samu a yankin.
“Tun daga ranar 19 ga watan Yuni, tsarin Rasha da rundunonin soji tare da haÉ—in gwiwar rukunin Æ™ungiyoyi na biyu na Æ™ungiyar sa kai na jama’ar Jumhuriyar jama’ar Luhansk (LPR) tare da goyon bayan rukunin sojojin kudancin, sun kai wani farmaki domin ‘yantar da yankin Jamhuriyar Jama’ar Luhansk,” in ji Shoigu.
Shoigu ya kara da cewa, an kewaye yankin “Gorsky cauldron”, Lysychansk da Severodonetsk cikin makonni biyu, kuma ana zargin sojojin Ukraine sun yi asarar sojoji 5,469 a fadan.
Putin ya gaya wa Shoigu cewa, sojojin da suka ba da gudummawar fada a LPR, za a ba su lada saboda “jajin cewar su,“kuma yanzu ya kamata su huta.”