Shugaban ƙasar Rasha, Vladimir Putin, ya halarci bikin faretin ranar nasara da Rasha ke gudanarwa kowacce shekara a Moscow, yayin da yake kokarin gangamin neman goyon bayan al’umma kan yakin da yake yi da Ukraine.
Dubban sojoji ne ke fareti da wasa da jiragen sama na yaki ciki har da jirgin da Mista Putin zai yi amfani da shi idan aka samu rikici na nukiliya, a lokacin bikin na murnar nasarar da tarayyar Soviet ta samu kan ‘yan Nazi a Jamus a 1945.
A jawabin da Putin ya gabatar a wurin ya bayyana Nato a matsayin barazana ga tsaron Rasha.
Shugaban ya ce suna yaki ne, domin al’ummar Donbas da tsaron Rasha, inda ya kwatanta mayakan Donbas din da na Soviet da suka yi galaba a yakin duniya na biyu.
Kasashen Yamma sun ce mamayar da Mista Putin ya yi a Ukraine abin kunya ne ga Rasha da tarihin da al’ummarta suka kafa.
Shugaba Vlodymyr Zelensky kuwa cewa, ya yi, luguden wuta da Rasha ke yi musu a birane da kwaso mutanensu fararen-hula ba shi da maraba da muggan ayyukan da Nazi suka tafka.