Shugaban Rasha Vladimir Putin, ya tattauna da sabon shugaban Iran na riƙon ƙarya Mohammad Mokhber, inda ya bayyana marigayi Raisi a matsayin abokin hulɗa nagari.
Fadar Kremlin ta tabbatar da tattaunawar ta su ta wayar tarho, wanda ɓangarorin suka jaddada aniyarsu ta yauƙaƙa alaƙa tsakanin Iran da Rasha.
Kamfanin labarai na Reuters ya ruwaito cewa, Iran babbar ƙawar Rasha ce, ta fannin ayyukan sojoji, tun bayan da Rashar ta ƙaddamar da hare-hare kan Ukraine a 2022.
Tun da farko, Putin ya bayyana alhininsa bayan ɓullar labarin rasuwar Shugaba Raisi a hatsarin jirgin sama samfurin mai saukar ungulu.
Putin ya bayyana marigayin a matsayin cikakken abokin Rasha kuma ƙwararren ɗan siyasa.