fidelitybank

Putin ne ya kashe miji na – Matar Navalny

Date:

Yulia Navalnaya, uwargidar jagoran ƴan adawa na Rasha Alexi Navalny ta ce shugaban Rasha, Vladimir Putin ne ya kashe mijin nata.

Ta faɗi hakan ne a wani jawabi da ta yi ta bidiyo.

Ta ce, “Ya kamata a ce Navalny ne a nan wurin da na zauna. Amma Vladimir Putin ya kashe shi.”

“Putin bai kashe Navalny a matsayin mutum kawai ba amma yana so ya kashe begenmu da ‘yancinmu, da kuma makomarmu”

“Mun san ainihin dalilin da ya sa Putin ya kashe Navalny kwanaki uku da suka wuce. Za mu gaya muku nan ba da jimawa ba.” in ji ta

“Amma, abu mafi mahimmanci da za mu iya yi wa Navalny da kanmu shi ne ci gaba da fafutika.”

“Zan ci gaba da aikin da Alexei Navalny ya fara, zan ci gaba da gwagwarmaya domin kasarmu. Kuma ina kira ga dukkan ku da ku tsaya tare da ni.”

“Ina kuma rokon ku da ku nuna fushi da ƙiyayya ga waɗanda suka yi ƙoƙari su kashe makomarmu.”

Putin dai har yanzu bai ce komai ba game da mutuwar Navalny.

bbc news nigeria today live

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp