A yau Talata ne Shugaba Putin na Rasha zai kasance mai masaukin baƙi ga tawagogi daga ƙasashe 36 waɗanda za su halarci taron ƙungiyar ƙasashen da arziƙinsu ke bunƙasa BRICS.
Fadar gawamnatin Rasha, Kremlin ta ce babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya ma zai halarci taron, kodayake mai magana da yawun Antonio Guterres ba bayar da tabbacin hakan ba.
Daga cikin shugabannin da aka gayyata akwai, Xi Jinping na China, da Firaministan India Narendra Modi da shugaban Iran Masoud Pezeshkian.
Moscow ta ce taron wata shaida ce da ke nuna cewa ƙoƙarin da ƙasashen yammacin Turai ke yi na mayar da Rasha saniyar-ware saboda mamayar da ta yi a Ukraine ya ci tura.
Ana ganin fadar Kremlin za ta matsa lamba don ƙulla yarjejeniya kan sabon tsarin hada-hadar kuɗi tsakanin ƙasashen waɗanda babu ruwansa da dalar Amurka.