Shugaba Biden na Amurka ya zargi shugaban Rasha, Vladimir Putin, da aikata “kisan ƙare-dangi a Ukraine.
Mista Biden ya bayyana hakan ne a karon farko a lokacin da yake jawabi kan farashin man fetur a Iowa.
“Na bayyana shi da kisan ƙare-dangi saboda a bayyana take ƙarara cewa, Putin na kokarin kawar da duk wani ɗan Ukraine daga doron-kasa,” in ji shi.
Biden ya ce, hujjojjin da ke tabbatar da hakan su ne karuwar aika-aika da Rasha ke yi, wanda ba su da maraba da kisan kare-dangi.
Sai dai kuma ƙasar Rasha ta musanta wadannan zarge-zarge.