Kungiyar masu samar da ruwan leda (ATWAP) ta kara farashin ruwan leda daya zuwa Naira 300.
Shugabar kungiyar, Clementina Ativie, ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba.
An cimma wannan matsaya ne baki daya a yayin taron kungiyar ATWAP na kasa a Abuja.
Ativie ta bayyana cewa, karin ya samu ne sakamakon farashin kayan da ake samu a halin yanzu da kuma yanayin tattalin arzikin Najeriya.
“Farashin ruwan buhun da aka fi sani da Pure water yanzu ya koma Naira 300 kan kowace leda kamar yadda farashin kamfanin ya ke.
Ta ce sabon farashin zai taimaka musu wajen ci gaba da biyan kudi da ci gaba da kasuwanci.
Sanarwar ta yi kira ga ‘yan kasa da su kasance masu fahimta da hakuri da kungiyar.
ATWAP ta kara farashin kudin ruwan na Pure Water zuwa Naira 200 a ranar 11 ga Nuwamba, 2021.