A ranar Lahadi ne Paris Saint-Germain ta kammala siyan mai tsaron ragar Barcelona Arnau Tenas.
Tenas ya koma zakarun gasar Ligue 1 ta Faransa kan kwantiragin shekaru uku.
“Na yi matukar farin ciki da shiga wannan babban kulob din da kuma kasancewa cikin dangin masu tsaron gida na PSG,” in ji Tenas bayan ya koma PSG.
Tenas ya zo ta makarantar La Masia ta Barcelona amma ya kasa buga wasan farko a Camp Nou.
Dan wasan na Spain U21 zai yi fatan buga wasa a karon farko karkashin kocin PSG Luis Enrique.