Mai horas da ƙungiyar Wolverhampton Wonderers, Bruno Lage, ya lashe kyautar masu horas wa na Barclays na watan Janairu na 2022.
Kocin Wolverhampton Wanderers ya fara horas wa na ban sha’awa a gasar Premier, kuma ya jagoranci kungiyarsa zuwa ga nasara a dukkan wasanni ukun da suka buga a watan Janairu, inda ya samu lambar yabo da Lage a karon farko ya lashe.
Ya ce, “Ina alfahari sosai, saboda wata ne mai kyau a gare mu” .
“Kwallon da kungiyar tayi, ya yi kyau sosa,i kuma mun samu nasara sau uku.” in ji Lage.
Daya daga cikin nasarori uku da Wolves ta samu a watan Janairu ita ce ta farko a gasar Premier a Old Trafford, kuma Lage ya samu nasarar 1-0 a Manchester United.