‘Yan majalisar dokokin Poland, sun kada kuri’a kan wani kudiri na ayyana kasar Rasha a matsayin kasar ‘yan ta’adda sakamakon yakin da ta ke yi a Ukraine.
Kudurin wanda ya gudana a ranar Larabar da ta gabata ya samu kuri’u 85, inda ya kara da cewa ya yi kakkausar suka ga cin zarafi na Rasha.
Idan za a iya tunawa dai gwamnatin kasar Rasha karkashin Vladimir Putin ta mamaye kasar Ukraine a ranar 14 ga watan Fabrairun wannan shekara, wanda ya kai ga kazamin yakin da ya yi sanadin mutuwar daruruwan mutane da kuma tasirin tattalin arzikin duniya.
A farkon wannan watan, Putin ya kuma ba da sanarwar shigar da yankuna hudu na Ukraine cikin Rasha. Matakin da shugabannin duniya da dama suka yi Allah wadai da shi.
Sai dai ‘yan majalisar dokokin kasar Poland sun yi kira ga dukkan kasashen da ke goyon bayan zaman lafiya da dimokuradiyya da ‘yancin dan Adam da su amince da hukumomin Tarayyar Rasha a matsayin gwamnatin ‘yan ta’adda.
‘Yan majalisar a yayin da suke zartar da kudurin, sun bayyana bayanan azabtarwa, korar da aka yi musu tilas, da kisan fararen hula da kuma kai hare-hare da gangan kan wuraren farar hula, domin nuna goyon bayansu ga kiran da suka yi na bayyana Rasha a matsayin kasa mai daukar nauyin ta’addanci.
“Mun san duk wadannan ayyukan ta’addancin gwamnati da kyau daga litattafan tarihi,” in ji sanarwar da ke kunshe da kudurin.