Paul Pogba zai bar Manchester United a kyauta idan kwantiraginsa ya ƙare a ƙarshen wannan kakar, kamar yadda kungiyar ta tabbatar.
Ɗan wasan na Faransa wanda ya ci kofin duniya mai shekara 29, ya ja kulob ɗinsa United ya kashe fam miliyan 89 a lokacin da ya koma can daga Juventus a 2016.
Ya ci ƙwallaye 39 a wasanni 226 da ya buga a zamansa na biyu a Old Trafford.