Kano Pillars za ta fafata a gasar share fage da za a yi a Katsina daga karshen wannan makon.
Za a gudanar da gasar ne daga ranar 30 ga watan Satumba zuwa 4 ga watan Oktoba.
Katsina United, Niger Tornadoes, Wikki Tourists, Doma United, El-Kanemi Warriors da Jigawa Golden Stars su ne sauran kungiyoyin da za su halarci gasar share fage.
Gasar dai na da nufin karfafa shirye-shiryen kungiyoyin ne na sabuwar kakar wasan kwallon kafa ta Najeriya.
Wanda ya lashe gasar zai samu tsabar kudi N1m, yayin da wadanda suka zo na biyu za su samu N500,000.
Kano Pillars dai ba ta yi rashin nasara ba a wasanni hudu da ta buga a baya.
Sai Masu Gida ya samu nasarar zuwa NPFL ne bayan ya zo na biyu a gasar NNL Super Eight a Asaba.