Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, ta kafa sabbin kwamitoci guda takwas domin tafiyar da harkokin kungiyar.
Kwamitocin sune Walwala da gudanarwa da yada labarai da bangaren Addu’o’i tare daTallace-tallace, Shawarwari da Kwamitin Æ™ungiyoyin ‘yan kasa da U-15.
Shugaban hukumar gudanarwar kungiyar Babangida Umar Little ne ya kaddamar da kwamitocin a Kano.
Babangida ya ce kwamitocin za su kasance karkashin jagorancin mambobin hukumar.
Ya bukace su da su yi aiki bisa ka’idojin da aka shimfida.
Kano Pillars za ta kara da Plateau United a filin wasa na Sani Abacha ranar Lahadi.


