Ɗan takarar shugaban ƙasa da aka kammala a watan jiya a ƙarƙashin jam’iyyar Labour Peter Obi, ya shigar da ƙara a hukumance, inda yake ƙalubalantar sakamakon zaɓen shugaban ƙasar da ya bai wa Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC nasara.
Mista Obi ya shigar da ƙarar ne a kotun sauraron korafe-korafen zaɓen shugaban ƙasa da ke Abuja a ranar Litinin.
Hukumar zaɓen ƙasar dai ta sanar da Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC mai mulkin ƙasar a matsayin wanda ya lashe zaɓen da aka gudanar.
Masu sa ido kan zaɓen na cikin da wajen ƙasar dai sun ce zaɓen na cike da kura-kurai.
Hukumar INEC ta tabbatar da cewa an samu matsala wajen amfani da na’urorinta, wanda kuma ya shafi aikewa da sakamakon zaɓen zuwa shafinta na yanar gizo.
Mai magana da yawun kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar ta Labour, Yunusa Tanko, ya shaida wa BBC a ranar Talata cewa cikin abubuwan da suke ƙalubalanta dangane da zaɓen sun haɗa da rashin cancantar shiga zaɓe na ɗan takarar jam’iyyar APC.
“Ɗan takararmu ya gabatar da ƙorafe-ƙorafe da dama gaban lauyoyi. Abu na farko shi ne rashin cancantar tsayawa zaɓe na ɗan takarar jam’iyyar APC. Kundin tsarin mulki ya yi tanadin cewa sai mutum yana da takardun makaranta kafin ya tsaya takara. Akwai kuma tuhumar da ake masa a Amurka,” in ji mista Yunusa.
Ya kuma ce ana aza ayar tambaya kan yadda aka gudanar da zaɓen da kuma sanar da wanda ya yi nasara da INEC ta yi.
Peter Obi shi ya zo na uku a zaɓen da aka gudanar yayin da ɗan takarar jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya zo na biyu.
Dukkansu dai suna kalubalantar sakamakon zaɓen saboda zargin da suka yi na cewa yana cike da kura-kur