Mataimakiyar shugaban jam’iyyar LP, Ladi Iliya, ta ce, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Peter Obi, yana karbuwa sosai a Arewacin Najeriya kamar yadda takwarorinsa na PDP da APC.
Ladi ta bayyana hakan ne a ranar Alhamis a garin Jos na jihar Filato, yayin wani taron gangami na kwana daya da wayar da kan masu ruwa da tsaki da kungiyoyin goyon bayan jam’iyyar Labour tare da kulla alaka tsakanin kungiyoyin tallafi da kungiyar kwadago ta Najeriya NLC.
“Muna nan ne domin mu hada kai da hada dukkan kungiyoyin goyon bayan Peter Obi da sauran kungiyoyin masu sha’awa domin mu yi magana da sauran kungiyoyin masu sha’awa. Ba wai muna yin haka ne kawai a Jihar Filato ba, muna tafiya a duk fadin kasar nan,” inji ta.
“Muna da hukumar siyasa ta NLC kuma ya kamata ta kula da ayyukan dukkanin kungiyoyin tallafi domin mu ci gaba da kasancewa tare da hadin kai.”