fidelitybank

PDP za ta tantance ‘yan takarar shugaban kasa 17 da suka sayi fom

Date:

‘Yan takarar shugaban kasa 17 a karkashin jam’iyyar PDP za su san makomarsu a yau, yayin da za su fuskanci kwamitin tantance su, domin tantance cancantarsu ko akasin haka.

An shirya gudanar da atisayen ne a sakatariyar jam’iyyar ta kasa da aka fi sani da Legacy House da ke Maitama, Abuja.

Duk ‘yan takarar da suka biya Naira miliyan 40, domin nuna sha’awa da kuma siyan fom din tsayawa takarar jam’iyyar maza ne, sai dai guda daya da ya biya Naira miliyan 5 kacal a wani mataki da shugabannin jam’iyyar suka tsara domin karfafa gwiwar mata.

‘Yan takarar su ne Teriela Oliver Diana, mace daya tilo; tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar; tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi; Gwamna Nyesom Wike (Rivers), Udom Emmanuel (Akwa Ibom), Bala Mohammed (Bauchi) da Aminu Tambuwal (Sokoto); tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki da tsohon sakataren gwamnatin tarayya Anyim Pius Anyim.

Sauran ‘yan takarar sun hada da tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose; tsohon Manajan Darakta na FSB, Muhammed HayatuDeen; Likitan da ke zaune a Amurka, Nwachukwu Anakwenze; hamshakin dan jarida, Dele Momodu; wani mai harhada magunguna, Sam Ohuabunwa; tsohon kakakin majalisar dokokin Abia, Cosmos Ndukwe da Charles Ugwu da Honorabul Chikwendu Kalu.

Tuni dai ‘yan takarar suka kara zage damtse wajen ganin sun samu goyon bayan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar musamman wakilan zabe a babban taron kasa da ke tafe.

nnn news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp