Shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Iyiochia Ayu, a ranar Talata, ya bayyana kwarin gwiwar cewa, jam’iyyar da dan takararta na shugaban kasa, Atiku Abubakar, a cikin sa’o’i 48 masu zuwa, za su gabatar da mataimakin dan takarar da zai yi takara.
Ayu ya bayar da wannan tabbacin ne a jawabin bude taron da ya yi da mambobin kwamitin tuntuba da aka kafa, domin taimakawa Atiku wajen zaben wanda zai yi takara.
Ya bayyana cewa, taron na ci gaba da tuntubar juna da nufin kaiwa ga zabin da ‘yan Najeriya za su yi murna da zabar mataimaki.
Ayu ya ce, “ zamu sanar da mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyarmu nan da sa’o’i 48.


