fidelitybank

PDP za ta rasa amanar ‘yan Najeriya idan ta sabawa sashe na 7 – Olabode George

Date:

Gabanin zaben shugaban kasa na 2023, tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na kasa Cif Olabode George, ya gargadi jam’iyyar adawa da su yi watsi da ra’ayin yin tsarin shiyyar da jam’iyyar ta yi.

George, wanda ya yi wannan gargadin a lokacin da ya gana da wasu ‘yan jarida a Legas ranar Juma’a, ya dage cewa, PDP za ta rasa amanar ‘yan Najeriya idan ta sabawa sashe na 7 karamin sashe na 3 (c) na kundin tsarin mulkin jam’iyyar.

Sai dai kuma Gwamnan jihar Ondo wanda ya taba zama gwamnan mulkin soji, ya kuma yi gargadin cewa, jam’iyyar za ta yi asara matuka, musamman a zabe mai zuwa, idan har ta kasa sanya tikitin takarar shugaban kasa a yankin Kudancin kasar nan.

Jigon na PDP ya lura cewa, bisa tsarin adalci, dole ne jam’iyyar adawa ta yi abin da ya dace, kuma a cewarsa, ke ware tikitin takarar shugabancin jam’iyyar zuwa yankin Kudu.

Ya kuma bukaci shugabannin jam’iyyar da su fito da tabbatacciyar sanarwa cewa, za a mayar da shugabancin jam’iyyar zuwa Kudu, yana mai cewa ta haka ne kawai jam’iyyar za ta sake samun amincewar ‘yan Nijeriya.

hausa

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp