Wani jigon jam’iyyar PDP, Bode George, ya bayyana fatansa na komawar jam’iyyar kan ganiya.
George ya sha alwashin tabbatar da cewa jam’iyyar PDP ta dawo da martabarta, don haka ya bukaci mambobin su dage.
Rikici ya kunno kai daga jam’iyyar PDP bayan da dan takararta na shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana tsohon gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, a matsayin abokin takararsa a zaben 2023.
Matakin da Atiku ya dauka ya sa tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya jagoranci gwamnonin G-5 da wasu jiga-jigan jam’iyyar suka bukaci tsohon shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata Iyorchia Ayu ya yi murabus.
Kiran da suka yi na cire Ayu shine don a samu daidaiton yankin tunda shi da Atiku duk ‘yan Arewa ne.
Sai dai George ya ce za a yi kokarin ciyar da PDP gaba.
Da yake jawabi a babban taron jam’iyyar PDP a Legas, George ya ba da tabbacin cewa duk da abin da ya faru a zabukan da ya gabata, ‘yan PDP su tsaya tsayin daka domin ba za a bar su su mutu ba.
Ya ce: “Ina roƙonku duka, da kuka kasance masu aminci, ku dage; za mu tabbatar da cewa jam’iyyar ta dawo da martabar da ta bata.”
Ya ba da tabbacin cewa, a lokacin da ya dace, dole ne shugabannin jam’iyyar na kasa su gudanar da “cikakkiyar binciken gawarwaki domin warware duk wasu matsalolin da suka shafi jam’iyyar.”