Wani tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, Reno Omokri, a ranar Litinin ya shawarci jam’iyyar PDP da ta dage zaben fidda gwani na shugaban kasa.
POLITICS NIGERIA ta rawaito cewa, Omokri ya ce, babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta Najeriya ta gudanar da zaben fidda gwani bayan jam’iyyar APC mai mulki.
Idan na ba PDP shawara, zan ba su shawarar dage zaben fidda gwani na shugaban kasa har sai APC ta yi nasu.
Jam’iyyar PDP ta tsayar da ranar 28 da 29 ga watan Mayu, yayin da ta APC ta tsayar da ranar 29 da 30 ga watan Mayu, wakilai 11,500 da aka zabo daga sassan kasar nan ne za su halarci zaben na jam’iyyun biyu. Yayin da APC ke da 7,800, ita kuwa babbar jam’iyyar adawa tana da wakilai 3,700.