fidelitybank

PDP ta yi watsi da matakin shugaban jam’iyyar da ya dauka

Date:

Kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP, ya yi watsi da matakin da shugaban jam’iyyar Iliya Damagum, ya dauka na soke taron kwamitin zartarwa na kasa (NEC) karo na 100 da aka shirya gudanarwa a ranar Litinin, 30 ga Yuni, 2025.

Haka nan kwamitin ya ce matakin da Damagum ya ɗauka na mayar da Samuel Anyanwu a matsayin sakataren jam’iyyar ba shi da tushe a kundin tsarin mulki na PDP.

A wata sanarwa da shugaban kwamitin amintattun, Sanata Adolphus Wabara ya fitar, ya bayyana cewa “kundin tsarin mulkin PDP na shekarar 2017 ya bayyana ƙarara cewa babu wani mutum ko ɓangare da ke da ikon soke ko ɗage taron shugabannin jam’iyya da aka yanke shawarar gudanarwa a taro na 99 da aka yi a ranar 27 ga Mayu, 2025”.

Saboda haka, matakin soke taron da Damagum ya ɗauka ya saɓa wa kundin tsarin jam’iyyar.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa “iƙirarin da Damagum ya yi na sake dawo da Sanata Anyanwu matsayin sakataren jam’iyyar ba ya da tushe.

Kwamitin ya ce har yanzu matakin da kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) ya ɗauka a zamansa na 600 na mika wa mataimakin sakataren jam’iyya, Arc. Setonji Koshoedo, riƙon muƙamin sakataren jam’iyyar shi ne sahihi.

Kwamitin ya kuma jaddada cewa “ba zai zuba ido yana kallon yadda wasu ke kokarin jefa jam’iyyar cikin rikici da rashin bin doka ba”.

Sanarwar ta bukaci dukkan ‘ya’yan jam’iyya da su girmama tsarin mulki da bin dokokin da suka kafa jam’iyyar domin kiyaye martaba da zaman lafiyarta.

assu today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

An kashe kwamandan Boko Haram a tafkin Chadi

Sojojin Jamhuriyar Nijar sun sanar da kisan wani jagoran...

Hisbah za ta yi wa ‘yan Daban Kano aure

Rundunar Hisbah ta jihar Kano ta sanar da wani...

Ganduje ya dawo Najeriya bayan ya shafe wata guda a Landan

Tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Ganduje,...

Barrister Sa’idu ya kama aiki bayan ya maye gurbin Muhyi Magaji

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya rantsar...

An ceto Mutane 26 da kwale-kwale ya kife da su a Sokoto

An samu nasarar ceto mutum 29 bayan hatsarin kwale-kwale...

An ceto Mutane 26 da kwale-kwale ya kife da su a Sokoto

An samu nasarar ceto mutum 29 bayan hatsarin kwale-kwale...

Barau zai mayar da filin wasan BUK na zamani

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya...

Jami’ar Bayero ta Kano ta yi sabon shugaba

Farfesa Haruna Musa, ya karɓi ragamar shugabancin jami’ar Bayero...

Gwamnatin Kano ta amince Barau FC ta yi wasa a filin Sani Abacha

Gwamnatin Jihar Kano ta amince da kungiyar kwallon kafa...

Gwamnatin Tinubu na takalar Kwankwaso da fada – Buba Galadima

Jigo a jam'iyyar NNPP, kuma na hannun tsohon gwamnan...

Newcastle United ta dauki dan wasan tsakiya Jacob daga Aston Villa

Newcastle United ta sanar da daukar dan wasan tsakiya...
X whatsapp