Jam’iyyar PDP, ta share dukkanin kananan hukumomi 23 a zaben kansiloli da aka kammala ranar Asabar a Benuwe.
Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Benuwe (BSIEC), Mista Tersoo Loko, ne ya bayyana hakan a ranar Lahadin nan yayin da yake bayyana sakamakon a shelkwatar hukumar da ke Makurdi.
Loko ya ce, PDP ta yi nasara ne da doke All Progressive Grand Alliance (APGA) da Labour Party (LP) inda ta lashe dukkan kujerun kansiloli baya ga kujeru 276 na kansiloli.
Ya godewa tawagarsa bisa gudanar da sahihin zabe da aka gudanar tare da bayyana cewa, wannan shi ne zabe na karshe da zai gudanar a matsayinsa na shugaban BSIEC.
Ya kuma godewa al’ummar Binuwai bisa goyon bayan da suka ba su, kuma ya yi farin ciki da cewa, ba a samu wani tashin hankali a kowane rumfunan zabe ba.