fidelitybank

PDP ta nada Tambuwal a matsayin babban daraktan yakin neman zabe Atiku

Date:

Babbar jam’iyyar hamayya ta PDP ta kafa kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa, inda ta nada gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal a matsayin babban daraktan yakin neman zaben shugaban kasar.

A wani sako da jam’iyyar ta wallafa a shafinta na Tuwita ta ce kwamitin wanda gwamnan jihar Akwa Ibom Udom Emmanuel ke shugabanta ya kunshi wasu gwamnonin da suka hada da gwamnan Ribas Nyesom Wike wanda ke ta kiraye-kirayen shugaban jam’iyyyar na kasa ya sauka daga mukaminsa.

Jam’iyyar dai ta fada rikicin cikin gida ne tun bayan zaben fitar da gwani na jam’iyyar, zaben da ya bai wa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar nasara, matakin da bai yi wa gwamnan jihar Ribas Nyensom Wike dadi ba.

A makon da ya gabata ne dai Tambuwal, wanda ke shugabantar kungiyar gwamnonin jam’iyyar, da shugaban kwamitin amintatu na jam’iyyar Sanata Walid Jibrin, suka ajiye mukamansu, matakin da suka ce sun dauka domin samun masalaha a jam’iyyar.

nigeria news(punch)

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp