fidelitybank

PDP ta mutu za mu binne ta a zaben gwamna – LP

Date:

Dr Alex Otti, dan takarar gwamna na jam’iyyar Labour Party LP, a jihar Abia, ya bayyana cewa jam’iyyar PDP ta mutu kuma za a binne ta a rumfunan zabe ranar 11 ga watan Maris.

Ya yi wannan jawabi ne a wani liyafa da gidauniyar CY Nwankwo ta shirya domin karrama shi wanda ya gudana a karamar hukumar Isiala Ngwa ta jihar Abia a karshen mako.

Otti ya yi takama da cewa jam’iyyar Labour ta kashe PDP, bayan da ta lashe daya daga cikin kujerun sanatoci uku da kuma kujeru shida na majalisar wakilai a jihar Abia a zaben ‘yan majalisun tarayya da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta gudanar a ranar 25 ga Fabrairu, 2023.

Karanta Wannan: Muna da shaidar cewa Obi ne ya lashe zabe – LP

Da yake bayyana jam’iyyar LP a matsayin jam’iyyar da ke kan gaba a jihar Abia, ya kuma kara da cewa PDP a yunkurinta na darewa kan karagar mulki ta tafi gari da farfaganda a kansa.

Kalamansa: “Idan kuka saurara, za ku ji duk abubuwan da ke fitowa daga wannan gwamnatin jihar ta PDP. Yadda za su haifar da tashin hankali, yadda za su tabbatar da cewa ba za a yi zabe ba, yadda za su rubuta sakamakon, yadda za su yi amfani da kudi da sayen kowa da kowa da sauran su. ”

Ya ci gaba da cewa: “Sun kuma yi gaba wajen sake nada wasu bata gari da suka kora a baya (ciki har da shugaban kwamitin rikon kwarya na kananan hukumomi).

“Ina tsammanin suna mayar da martani kamar mutumin da ke nutsewa. Amma sun riga sun nutse kuma za mu binne su a ranar 11 ga Maris 2023.”

Otti ya kara da cewa: “Idan kun duba sararin samaniyar kafofin sada zumunta, duk abin da suke yi yanzu shine fitar da rahotannin karya da ake zargin suna fitowa daga gare ni. Daya daga cikin abubuwan da suka fada shi ne, zan kori yawancin ma’aikatan gwamnati.

“A gaskiya, wadanda gwamnati ta nada ne ke yawo a kafafen sada zumunta daban-daban

legit com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Zan cigaba da sa yawan jini ga maƙiya Tinubu – Wike

Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya sha alwashin...

Tinubu zai magantu a kan ranar Dimokradiyya

Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, zai yi jawabi ga...

A shirye nake na mutu don nasarar APC a 2027 – Orji Kalu

Sanatan Abia ta Arewa, Orji Uzor Kalu, ya bayyana...

Bayan hutun Sallah Tinubu zai koma Abuja

Shugaban ƙasa, Bola Tinubu na kan hanyarsa ta komawa...

Mutane 570 aka kashe a Najeriya cikin watan Afrilu – Rahoto

Hukumar kare haƙƙin ɗan'adam a Najeriya ta ce, adadin...

PDP ba za ta mutu ba duk da rikicin cikin gida – Wike

Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya ce...

Sojoji sun kashe riƙaƙen ɗan bindiga Guddel a Kaduna

Sojoji sun yi nasarar kawar da fitaccen shugaban ‘yan...

Fadar shugaban ƙasa ta yi kakkausar gargaɗi a kan Ndume

Fadar shugaban kasa ta yi kakkausar gargadi ga dan...

Kare Ya Kashe Ragon Layya: Mai ƙwacen waya ya kashe Sojin ruwa a Kaduna

Wani mai ƙwacen waya ya kashe wani soja bayan...

Sojoji sun hallaka ƴan Boko Haram da dama

Da sanyin safiyar ranar Litinin, dakarun rundunar Haɗin kai...

Tarzomar kama baƙin haure a Amurka na yamutsa hazo

An shiga rana ta uku a tarzomar da ake...

Alhazai sun kammala aikin Hajji bana

A ranar Lahadin da ta gabata ne alhazai miliyan...
X whatsapp