fidelitybank

PDP ta kori wasu ‘yan takara biyu bayan tantance su

Date:

Kwamitin tantance ‘yan majalissar dokokin jam’iyyar PDP a jihar Kogi, ya kori Ubolo Itodo Okpanachi da Aminu Abubakar Suleiman daga takarar Sanatan Kogi ta Gabas bisa wasu ayyuka na rashin da’a.

Sakamakon tantancewar da aka fitar a ranar Alhamis a Lokoja, babban birnin jihar, ya nuna cewa, yayin da Isaac Alfa da Victor Adoji suka samu takardar amincewar kwamitin don ci gaba da neman kujerar sanata, Suleiman da Okpanachi an hana su shiga takarar.

Suleiman dai an tantance shi ne kuma ba shi da rajista katin jam’iyya a yankin majalisar dattawa, don haka bai cancanci shiga zaben Sanata ba.

An ce kwamitin ya lura da cewa rashin cancantar kada kuri’a ko kuma shiga zaben ‘yan majalisar dattawa, kai tsaye ya toshe damarsa na cin gajiyar duk wata kuri’a da aka kada a gundumar. Suleiman, ya kara da cewa kwamitin bai zabi kowa ba a Kogi ta gabas don haka bai cancanci tsayawa takara ba.

A daya bangaren kuma, Okpanachi, ba’a wanke shi ba, saboda zarginsa da hannu a cikin ayyukan kin jinin jam’iyya da kuma tarin wasu korafe-korafe da ke kalubalantar cancantar sa na tsayawa takara.

Ana zargin sa da zama dan jam’iyyar APC, jam’iyyar da aka ce ya koma, kuma a wani lokaci aka ba shi mukami.

dailypost news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp