fidelitybank

PDP ta jinjina wa sojojin Najeriya a fagen daga

Date:

Jam’iyyar hamayya ta PDP, ta jinjina wa sojojin Najeriya, bisa jajircewa da sadaukar da kai da su ke yi a ƙasar nan, musamman a lokacin da ta fuskanci tabarbarewar tsaro a cikin shekaru shida da suka gabata.

Jam’iyyar PDP ta yi na’am da irin bajinta da kishin kasa da jiga-jigan sojojin ke yi a fagen daga, wadanda duk da kalubalen da ake fuskanta a kullum, suna jefa rayuwarsu cikin kangi, inda da yawa suke rasa rayukan su, domin hadin kai da tsaron Najeriya.

PDP ta bayyana hakan ne a lokaci bikin tunawa da ƴan mazan jiya wanda aka gudanar a ranar Asabar.

Jam’iyyar PDP, ta kuma bukaci gwamnati ta dauki matakin samarwa sojojin isassun kayan aiki tare da inganta jin dadin sojojin, domin tabbatar da ingancin aikinsu ga ƙasa.

Ta ce, “Jam’iyyar mu kira ga gwamnati da ta tabbatar da jin dadin iyalan jaruman mu wadanda suka sadaukar da rayukansu, domin al’ummarmu. Kar a bar iyalansu da ‘yan uwansu su ci gaba da shan wahala”. A cewar PDP.

Jam’iyyar PDP ta kuma bukaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da bayar da goyon baya da kuma yi wa sojoji addu’a a babban aikinsu na kare ƴan Najeriya.

legit nigeria news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp