Shugabani da gwamnonin da sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP na ci gaba da tattanawa wajen gani sun shawo kan ɓarakar da ta kunno kai a tsakaninsu da ya janyo tsaiko, wajen gudanar da taron majalisar zartawa na jam’iyyar da aka shirya gudanarwa a yau Litinin.
Tun da safiyar yau ne dai aka ga jami’an ‘yansanda da na tsaron fararen hula na Civil Defense suka yi wa ofishin jam’iyyar na Wadata Plaza, Abuja tsinke tare da hana dukkanin manyan jami’an jami’yyar shiga.
Yanzu haka dai kwamitin amintanntu na jam’iyar na gudanar da wani taron sirri a babban ɗakin taro na Ƴar’adu Center da ke Abuja.
Taron nasu na zuwa a daidai lokacin da gwamnonin jam’iyyar da ƴan majalisar dattawa da na wakilai da ke gudanar da wani taron a gidan gwamnatin jihar Bauchi da ke unguwar Asokoro a birnin na Abuja.
Wakilin BBC da ke wurin ya ce duka tarukan biyu ana yi ne da nufin lalubo bakin zaren yadda za a gudanar da babban taron kwamitin zartarwa na jam’iyyar (NEC) da ake shirin yi a ofishin jam’iyyar da ke Wadata Plaza.
Tun da faro dai kwamitin Amintattun Jam’iyyar sun shirya gudanar da taron nasu ne a ofishin jam’iyyar da ke Wadata Plaza da misaƙalin ƙarsfe 10:00 na safe amma hakan bai samu ba.