Goyon bayan takarar gwamnan Rivers Nyesom Wike na ci gaba da karuwa, bayan amincewar tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa Cif Bode George da jam’iyyar PDP reshen jihar Legas.
Wike ya karbi bakuncin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar ne bayan ganawar sirri da ya yi da shugabannin jam’iyyar na Legas da sauran jiga-jigan jam’iyyar Kudu maso Yamma a ofishin Cif Bode George na Ikoyi a karshen makon da ya gabata.
Wanda ya halarci taron shine gwamnan jihar Oyo, Engr. Seyi Makinde; tsohon gwamnan jihar Benue, Sanata Gabriel Suswan; shugabannin jam’iyyar na yankin Kudu-maso-Yamma, Mista Soji Adagunodo, wanda shi ne mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa Kudu maso Yamma da dai sauransu.
Da yake bayyana goyon bayansa ga bayyanar Wike, Cif Bode George ya ce, ya mallaki mutunci da kuzarin samartaka don jagorantar kasar daga cikin halin da take ciki.
Ya ce: “Idan a na maganar gaskiya, idan ana maganar siyasa, idan ana maganar zama mai cikakken amfani, shi ne (Wike).”
“Har ila yau, yana da zurfin ƙuruciyarsa wanda zai iya gudu daga nan zuwa waccan ƙofar cikin daƙiƙa biyu, ba zan iya ƙara yin hakan ba. Kamar janar-janar soja ba mu yi ritaya ba, muna shuɗewa kawai. Amma muna bukatar matashi mai hazaka wanda zai dauke mu daga inda muke a yanzu ya kawo wa kasar nan sabon numfashi.”