fidelitybank

PDP ta gargaɗi Majalisa kar ta amince da kasafin Tinubu

Date:

Jam’iyyar PDP tayi watsi da kasafin kudin tarayya na Naira tiriliyan 47.9 na shekarar 2025 da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar a ranar laraba.

Jam’iyyar tana mai bayyana shi a matsayin “wanda ba zai yiwu ba, ba gaskiya ba, kuma cike da rashin bayyana gaskiya.”

A cikin wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na Kasa na PDP, Debo Ologunagba, ya fitar a ranar Laraba, jam’iyyar ta bayyana kasafin a matsayin wanda akayi ba don al’umma ba, tare da gargadin cewa aiwatar da shi zai kara tsananta matsalolin tsaro, talauci, da takaici a fadin kasa.

Tinubu ya gabatar da kasafin kudin 2025 ga yan Majalisar Dokokin Kasa, inda ya ware Naira tiriliyan 4.91 ga bangaren tsaro, Naira tiriliyan 4.06 don inganta ababen more rayuwa, Naira tiriliyan 2.48 ga bangaren kiwon lafiya, da Naira tiriliyan 3.52 don ilimi.

Jam’iyyar PDP tayi suka kan kasafin, tana zargin cewa ya cika da alkaluman tattalin arziki marasa tabbaci da alkawuran da ba su da tushe ko makama.

“Kasafin Naira tiriliyan 47.9 na tarayya na shekarar 2025 kasafi ne mai cin amanar al’umma, wanda idan aka aiwatar dashi, zai kara jefa kasa cikin matsalolin tsaro, talauci, da rashin fata,” in ji sanarwar.

Jam’iyyar PDP ta zargi gwamnatin Tinubu da rashin zuba jari mai ma’ana a bangarorin da suka hada da noma, wutar lantarki, man fetur, da kananan da matsakaitan masana’antu. Ta bayyana cewa wadannan bangarori ne tushen bunkasa tattalin arziki da tabbatar da kwanciyar hankali.

Haka kuma, PDP ta soki kasafin saboda rashin fayyace bayanai, musamman kan yadda za a raba kudade tsakanin ayyukan ci gaba da na yau da kullum.

PDP tayi kira ga Majalisar Dokoki ta Kasa da tayi watsi da kasafin kudin 2025 a yadda yake, tana amfani da ikon da doka ta bata don sake fasalta kasafin yadda zai mayar da hankali kan bunkasar tattalin arziki da jin dadin al’umma.

nigerianewspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Zulum ya miƙa kyautar Naira miliyan 100 ga iyalan Sojojin da aka kashe

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya bai...

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...

Musulman Nijeriya a cigaba da jajircewa – Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkarshin jam'iyyar Labour a...

Akwai takaici ambaliyar Neja – IBB

Tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Babangida, ya kwatanta ambaliyar...

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...

Isra’ila ta gano gawar ƴan ƙasarta

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta gano gawar ''yan...

Ma’aikatan wutar lantarki a Abuja sun fusata

Ma'aikatar kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja Electricity Distribution...
X whatsapp