Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, ya bayyana ra’ayinsa kan rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar PDP.
Fani-Kayode ya ce, aljani da shedan sun shigo PDP.
Ya yi magana ne a kan kalaman da jigo a jam’iyyar PDP, Bode George ya yi na cewa wata kila wani shaidani ya kutsa cikin jam’iyyar adawa.
George dai na mayar da martani ne kan rashin jituwar da ke tsakanin gwamna Nyesom Wike da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar.
Da yake kira gare su da su kwantar da hankalinsu, jigon na PDP ya ce da alama “wani irin shaidan” ya shigo jam’iyyar.
Da yake mayar da martani, Fani-Kayode ya jaddada cewa an damfari Wike da ’yan Kudu a PDP.
Da yake magana a gidan Talabijin na Channels, Fani-Kayode ya ce: “PDP ita ce jam’iyyar da ke wasa da aljanu a yau, a lokacin da suke ta fama da ta’addanci, sun damfari Wike da duk ’yan Kudu, har yanzu suna cewa babu abin da zai canza; cewa shugaban jam’iyyar ba zai sauka ba.


