Babbar jam’iyyar hamayya ta PDP, ta dakatar da tsohon gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose tare da wasu mutane uku ‘yan jam’iyyar.
Cikin wata sanarwa da jam’iyyar ta wallafa a shafinta na Twitter, ta ce ta dakatar da Sanata Pius Anyim da Farfesa Dennis Ityavyar da kuma Malam Aslam Aliyu na jihar Zamfara.
Sanarwar ta ce dakatarwar ta su za ta fara aiki ne nan take, wato a yau Alhamis 23 ga watan Maris.
Sanarwar ta kuma bayyana tura gwamnan jihar Benue Samuel Ortom gaban kwamitin ladabtarwa na jam’iyyar, kan zargin da ta yi masa na yaÆ™ar jam’iyyar ta Æ™arÆ™ashin Æ™asa.
“Bayan dogon nazari da muka yi kan harkokin jam’iyyarmu, kamar yadda kundin tsarin mulkin jam’iyyar na 2017 ya bayyana, mun tura gwamna Samuel Ortom na jihar Benue gaban kwamitin ladabtarwa na wannan jam’iyya, bisa rahoton da muka samu na yin zagon Æ™asa ga jam’iyyar tamu,”.
A ƙarshe ta nemi sauran mambobinta da su ci gaba da zama tsintsiya ɗaya maɗaurinki ɗaya, domin ci gabansu baki ɗaya.