Jam’iyyar PDP reshen jihar Osun ta dakatar da ayyukanta na tsawon mako guda bayan David Adeleke, dan gidan zababben gwamnan jihar, Ademola Adeleke, ya rasa dansa, Ifeanyi.
Shugaban riko na jam’iyyar PDP na jihar Osun, Adekunle Akindele, a cikin sakon ta’aziyya ga iyalan Adeleke a ranar Talata, ya bayyana rasuwar Ifeanyi, dan Davido da Chioma a matsayin wani lamari mai matukar bakin ciki.
Ya kuma umurci dukkan sassan jam’iyyar da kwamitoci da su dakatar da ayyukan domin ta’aziyya da iyali.
“Muna jimamin ficewar danmu Ifeanyi cikin bakin ciki. Muna addu’ar Allah ya jikan sa. Rana ce ta bakin ciki, amma mun dage da imaninmu ga Ubangijin talikai.
“Ta’aziyyarmu tana zuwa ga Davido, jakadan matasanmu. Muna mika ta’aziyya ga mahaifinmu, Dokta Deji Adeleke da dukan dangin Adeleke. Muna addu’ar Ubangiji Allah ya ba ‘yan uwa ikon jure wannan rashi maras misaltuwa,” a karshe sanarwar.
Labari ya fito da sanyin safiyar Talata, 1 ga Nuwamba, 2022, na mutuwar Ifeanyi mai shekaru uku.
An tattaro cewa ya nutse ne a wani wurin ninkaya da ke gidan mahaifinsa na tsibirin Banana.