Jam’iyyar PDP ta dage cewa ‘yan majalisar dokokin jihar Rivers 26 da suka bar jam’iyyar zuwa jam’iyyar APC, yanzu haka ba ta da wata alaka da su kuma ba ‘ya’yan jam’iyarta ba ne.
Mai baiwa jam’iyyar PDP shawara kan harkokin shari’a, Adeyemi Ajibade, SAN, ya shaida wa manema labarai jim kadan bayan mai shari’a Donatus Okorowo na wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ya dage sauraron karar ‘yan majalisar har sai ranar 24 ga watan Janairu, 2024.
Ajibade ya ce duk da shugaba Bola Tinubu ya taka rawa a rikicin da ke tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike wajen sulhunta su, amma jam’iyyar ta tsaya kan abin da kundin tsarin mulki ya ce kan batun sauya sheka.
A cewar babban lauyan, baya ga haka, kundin tsarin mulkin kasar nan ya bayyana sashe na 109 (1g) cikin baka, ya bayyana karara game da batun wanda ya ficce daga jam’iyya ya koma wata jam’iyyar.


