Jam’iyyar PDP ta gayyaci ministan babban birnin tarayya, FCT, Nyesom Wike, da ya gurfana a gaban kwamitin ladabtarwa kan wasu zarge-zargen cin zarafin jam’iyya.
Mataimakin sakataren yada labaran jam’iyyar PDP na kasa Ibrahim Abdullahi ne ya bayyana haka a wata hira da gidan talabijin na Channels a ranar Litinin.
A cewarsa, kwamitin ladabtarwa ya rubuta wa Wike wasika inda ya gayyace shi da ya bayyana a kan kalamansa na baya-bayan nan game da jam’iyyar.
Abdullahi ya ce furucin da ministan babban birnin tarayya ya yi game da “hana wuta a jihohinsu” game da gwamnonin PDP ba abu ne da za a amince da shi ba.
A cewarsa, “Ya kamata Wike ya iya sarrafa kalamansa a hankali; wannan magana ce mai ban takaici. Ba mu yi tsammanin zai faɗi haka ba, kuma ba ma tare da shi a kan haka, don mu faɗa muku gaskiya.”
Hakan na zuwa ne sa’o’i bayan Wike ya bayyana gamsuwarsa da yin aiki a karkashin Shugaba Bola Tinubu, duk da suka da kuma cece-ku-ce da aka yi a kan nadin nasa.
Ministan babban birnin tarayya ya bayyana cewa duk wanda ya fusata da mukaminsa a gwamnatin Tinubu ya je ya rungume taransfoma.