fidelitybank

PDP ta ɗage babban taron shugabanninta na ƙasa

Date:

Babbar jam’yyar hamayya ta PDP a Najeriya, ta sanar da ɗage babban taron shugabaninta a ƙasa karo na 99 da ta shirya gudanarwa ranar 28 ga watan Nuwamban da muke ciki.

Cikin wata sanarwa da babban sakataren jam’iyyar na ƙasa, Sanata Samuel Anyanwu ya fitar ranar Alhamis, ya ce an ɗage taron shugabannin jam’iyyar karo na 99 saboda jana’izar mai ɗakin gwamnan jihar Akwa Ibom, Patience Umo Eno da za a yi.

Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyya, ke samun saɓani da rikice-rikice tsakanin ‘ya’yanta.

Tun bayan da wata kotu ta sanar da cire shugaban jam’iyyar na ƙasa, Sanata Iyorchia Ayu a 2023, jam’iyyar ta sanar da naɗa Ilya Damagum a matsayin shugabanta na riƙo.

To sai dai shi ma Damagun ya riƙa fuskantar suka daga wasu ‘ya’yan jam’iyyar – waɗanda suka riƙa kiraye-kirayen ya sauya daga muƙamin.

A taronsu karo na 98 da suka gudanar cikin watan Afrilu, shugabannin jam’iyyar sun amince da kafa kwamitocin sasanto da na ladabtarwa da shirya tarukan jam’iyyar tun daga matakin mazaɓu zuwa jihohi.

jalingo news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp