A yau ne babbar jam’iyyar adawa a Najeriya, PDP ke gudanar da taron majalisar zartaswarta na ƙasa karo na 98.
An soma taron ne da na kwamitin amintattu na jam’iyyar kafin a ɗora da na majalisar zartaswar a hedikawatar jam’iyyar da ke Abuja.
Taron na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyar ke fuskantar rikicin cikin gida.
Ƙusoshin jam’iyyar daga sassa daban-daban na Najeriya ne ke halartar taron.
Ga wasu hotuna da muka samu daga wurin taron.