Jam’iyyar PDP ta tsara shirin lashe jihohi 25 bayan zaben gwamna a shekarar 2023.
Shugaban jam’iyyar na kasa, Dr Iyorchia Ayu, ne ya bayyana hakan a jiya a sakatariyar jam’iyyar PDP ta kasa a lokacin da jam’iyyar ke bayar da shaidar na tsayawa takarar gwamna a jam’iyyar.
Ayu, wanda ya ce, jam’iyyar PDP na shirin komawa kan hanyarta ta samun nasara, ya koka da cewa jam’iyyar da take da matsayi na da jihohi 13 ne kawai.
Da yake bayyana ’yan takarar gwamna a matsayin jajirtattu kuma masu aminci, sai dai ya bukace su da su yi sulhu da abokan hamayyar su a jam’iyyar. In ji Leadership.
“Mun yi imanin cewa PDP za ta koma hanyar samun nasara. A lokacin da muka fara a 1999, mun iya samar da gwamnoni 21, mun girma a 2003 zuwa 28 aka ci gaba da zama 28 har zuwa 2007.
“Abin takaici, mun shiga cikin mawuyacin hali kuma adadin ya ragu. A yau muna da gwamnoni 13 ne kawai, ga jam’iyyar siyasa irin wannan. Wannan bai isa ba.