Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na kasa na (Kudu maso Yamma), Bode George, ya gargadi jam’iyyar game da amincewa da taron da tsohon shugaban jam’iyyar na jihar Legas, Deji Doherty ya yi, yana mai cewa hukuncin kotu da aka yi masa na iya jawo wa jam’iyyar illa a zaben 2023.
A wata ganawa da manema labarai a ofishinsa da ke Ikoyi a ranar Litinin, George ya ce babbar kotun jihar Legas ta yanke hukunci a kan Doherty a bara tare da mayar da tsohon shugaban riko na jam’iyyar a jihar, Adegbola Dominic, a matsayin halastaccen shugaba. Ya ce idan jam’iyyar ta amince da zartaswar da aka samar a taron da Doherty ya yi, to tana iya yin kasadar faduwa zabe.
Ya kuma bukaci jam’iyyar PDP da ta dauke babban taronta na kasa da ya kamata a yi a ranakun 28 da 29 ga watan Mayu daga Abuja zuwa Legas saboda yadda jam’iyyar APC ma za ta yi nasu a wuri guda a ranakun 30 da 31.
“Yana da mahimmanci a nuna cewa kotun da ke da hurumi ta tsige Deji Doherty, don haka duk wani taron da zai yi ba shi da amfani a karkashin doka. Zai fi kyau a guje wa duk wani dan takarar da ya fito daga majalisar da ya gudanar ta yadda nan gaba ba wanda zai ce maka zaben ya saba wa doka.