Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya yi alfaharin cewa jam’iyyar PDP za ta lashe dukkan zabukan da za a yi a shekarar 2023 a jihar sa, ban da zaben shugaban kasa har sai an yi abin da ya dace.
Gwamna Wike ya bayyana haka ne jiya a Fatakwal yayin rantsar da sabbin jamiāan Hulda da Mazabu 319 da aka nada.
Ku tuna cewa Wike da dan takarar shugaban kasa na jamāiyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar sun shiga fafatawa a siyasance bayan faduwa daga zaben fidda gwani na jamāiyyar.
Gwamnan ya ce: āPDP ce za ta ci Jihar mu. Ba ina boyewa ba ne dangane da batun Gwamna da Majalisar Wakilai da Majalisar Dattawa da na Jiha. Dayan kuma (shugaban kasa) ba mu yanke hukunci ba, sai an yi abin da ya dace.
“Na kalli lokacin da wani Dr. Abiye Sekibo, yayin da yake jawabi ga mutane a gidansa jiya (Lahadi), ya ce shi darakta ne na magoya bayan Atiku a Rivers. Ba ni da wata matsala da hakan, amma ba shi da wannan damar na yin magana a madadin jihar Ribas,ā inji shi.