fidelitybank

PDP ce za ta ci zabe a Anambra – Okowa

Date:

Mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP kuma gwamnan jihar Delta, Sanata Ifeanyi Okowa ya ce, jam’iyyarsa za ta yi nasara a jihar Anambra, a zaben 2023.

Duk da rinjayen jam’iyyar All Progressives Grand Alliance, APGA, wacce ita ma ke da dan takarar shugaban kasa, da kuma jam’iyyar Labour Party, LP, wadda dan takararta, Mista Peter Obi ya fito daga jihar, Okowa ya ce PDP za ta karbe jihar.

Okowa wanda abokin takarar Atiku Abubakar ne ya wakilci garin Onitsha a bikin Ofala karo na 20 na basaraken gargajiya na tsohuwar Masarautar Obi Alfred Nnaemeka Achebe, wanda jagoran kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa a jihar Anambra, Farfesa Obiora Okonkwo, shugaba United Nigeria Airline.

Okonkwo wanda ya zanta da manema labarai yayin da yake wakiltar Okowa ya ce: “PDP ta shirya tsaf don yakin neman zabe. Anambra ta kasance gidan PDP, kuma kuna iya duba ta. A baya dai mun samu gagarumin rinjaye a dukkan zabukan shugaban kasa, kuma kusan a kowane lokaci, mun samu rinjaye a zaben ‘yan majalisun tarayya, kuma bana tunanin hakan zai bambanta.

“Kwamitin yakin neman zaben yana zuwa Anambra, kuma za mu yi yakin neman zabe a kowane lungu na jihar Anambra, daga kowane mai zabe, kowace rumfar zabe, kowace unguwa da kowace karamar hukuma.

“Ba ni da tantama cewa a karshen wannan rana, mutanen Anambra za su san cewa muna bukatar a sake hada mu da Abuja, kuma waya daya da za ta ba mu wannan alaka da harkar siyasa ita ce PDP.”

Da yake magana kan mamayar jam’iyyar All Progressives Grand Alliance, APGA a jihar Anambra, Okonkwo ya bayyana APGA a matsayin kawar PDP.

“APGA ita ce ke rike da jihar a lokutan baya lokacin da PDP ta samu kashi 95 na kuri’un jihar, duka a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da aka gudanar a jihar Anambra. Ina ganin haka zai kasance.

“Al’ummar Anambra sun kasance suna zabar PDP a kowane lokaci, kuma ina mamakin dalilin da ya sa kuke jin wannan lokacin zai bambanta. Muna da yakinin cewa za mu ci Anambra a karshen wannan rana.”

Ya kuma yabawa sarkin gargajiya na masarautar Onitsha, Obi Alfred Nnaemeka Achebe bisa gudanar da bikin al’adu na Ofala mai ban sha’awa, yayin da ya kuma bukaci sauran sarakuna da al’ummomi da su shiga baje kolin al’adun Afirka.

natforce 
latest news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp