fidelitybank

PDP a Kano ta ja hankalin Ganduje a kan sabunta lasisin makarantu

Date:

Jam’iyyar hamayya ta PDP a jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar, Dakta Abdullahi Umar Ganduje da kada ya sake ya yi amfani da batun soke rijistar makarantu masu zaman kansu wajen tatsar kudade daga masu makarantun da sunan sake tsarin makarantun.

A wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar mai dauke da sa hannun shugabanta na jihar, Shehu Wada Sagagi, wadda a ciki take nuna alhini bisa kisan yarinyar nan ‘yar shekara biyar Hanifa wadda shugaban makatantarsu ya sace tare da kashe ta, jam’iyyar ta kuma yaba wa jami’an tsaro kan yadda suka yi saurin ganowa tare da gurfanar da wadanda ke da hannu a lamarin a gaban kotu.

A kan matakin da gwamnatin jihar ta dauka na soke lasisin gudanarwa na dukkanin makarantu masu zaman kansu a jihar ne sakamakon abin da ya faru a kan yarinyar, jam’iyyar hamayyar ta ce duk da cewa abu ne da yake da kyau sake tsrain makarantun, to amma ta yi gargadi ga gwamnatin da kada ta yi amfani da wannan dama wajen tsatsar kudade daga masu makarantun.

Jam’iyyar ta bukaci gwamnatin jihar karkashin jagorancin Abdullahi Umar Ganduje da ta bi ka’idojin da doka ta gindaya na sanya ido tare da gudanar da makarantu masu zaman kansu wajen aiwatar da gyare-gyaren.

bbc nigeria news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp