Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong, ya ce, Fararoma Francis ba ya adawa da zamansa Darakta Janar na yaƙin neman zaɓen Bola Ahmed Tinubu na takarar Shugaban Ƙasa.
Lalong ya ce har yanzu shi cikakken Kirista ne ɗan ɗariƙar Katolita duk da hukuncin da ya yanke na jagorantar yaƙin neman zaben takarar shugaban ƙasa da matimakinsa a APC na Musulmi da Musulmi.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ƙungiyoyin kiristoci da yawa da ke adawa da tikitin takarar Musulmi da Musulmi sun yi wa Gwamna Lalong ca kan wannan jagoranci nasa.
Wasu ma sun yanke alaƙa da shi saboda a ganinsu ya bi sahun masu goyon bayan tikitin takarar Musulmi da Musulmci a shugaban ƙsa da mataimaki.
Amma Lalong a ranar Laraba ya ce hakan bai dame shi ba.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake amsa tamboyoyi daga manema labarai na fadar Shugaban ƙasa bayan ganawar sirri tsakaninsa da Shugaba Muhammadu Buhari a Abuja.
Lalong yace a matsayinsai na cikakken dan katolika mai bin aƙidun ɗarikar sau da kafa, har ma ya taɓa samun lambar yabo mafi girma, fafaroma ya ce masa babu wani laifi don ya jagoranci takarar Musulmai.


