Tsohon dan wasan kasar Jamus, Mesut Ozil, ya sanar da yin ritaya daga buga kwallo.
A cewar Ozil, ya dauki matakin ne saboda raunin da ya ji a baya-bayan nan.
Dan wasan mai shekaru 34 ya shafe shekaru uku a gasar Super Lig ta Turkiyya.
Ozil ya yi ritaya bayan ya buga wa Basaksehir wasanni hudu.
Ya tara wasanni sama da 500 a cikin aikinsa na shekaru 17.
“Bayan yin la’akari da hankali, ina sanar da murabus na nan da nan daga wasan kwallon kafa,” in ji Ozil a ranar Laraba.
Ya kara da cewa: “Tafiya ce mai ban mamaki cike da lokutan da ba za a manta da su ba.
“Ina so in gode wa kungiyoyi na Schalke, Werder Bremen, Real Madrid, Arsenal FC, Fenerbahçe, Basaksehir da kuma kociyoyin da suka goyi bayana, da abokan wasan da suka zama abokai.”