Gwamna Gboyega Oyetola na jihar Osun, ya gabatar da kasafin Naira biliyan 136,265,988.140 na kasafin kudin shekarar 2023 ga majalisar dokokin jihar.
Kiyasin kasafin kudin 2023, mai taken; “Budget of Consolidation” na kunshe da wata wasika daga gwamna Gboyega da majalisar ta karba a ranar 29 ga watan Satumba, daga hannun kakakin majalisar.
Majalisar ta koma aiki kan kididdigar kasafin kudin shekarar 2023 saboda muhimmancinta ga jama’a domin haduwa da da’irar kasafin kudin shekara.
Kakakin majalisar, Timothy Owoeye a cikin jawabinsa, ya lura cewa kiyasin kasafin kudin 2023 da aka yi wa lakabi da “Budget of Consolidation” ba shi da alaƙa da siyasa kwata-kwata.
Ya yi nuni da cewa kiyasin kasafin ya wuce siyasa ya ce batun kasafin ya dogara ne da tsarin mulki da ka’idoji.
Ya kuma yi nuni da cewa akwai bukatar gwamnan ya gudanar da ayyukansa kamar yadda kundin tsarin mulki da ka’idojin majalisar suka tanada.